Amurka ta sanar da kababa wa ministocin biyu da suka fito daga kungiyar Amal da kuma kungiyar Maradah ta kiristoci, bisa zarginsu da cewa suna da kyakkyawar alaka da kungiyar Hizbullah.
Amurka ta bayyana cewa, ministocin biyu sun rika kare manufofin kungiyar Hizbullah a cikin gwamnati da kuma majalisar dokokin kasar Lebanon, a kan haka takunkumin da Amurka ta kakaba wa Hizbullah ya hada har da su a halin yanzu.
Kungiyar Hizbullah dai tana amatsayin wani bababn gishiki a cikin harkokin siyasar Lebanon, kamar yadda kuma mayakan kungiyar ne suka kawo karshen mamayar Isra’ila a kan kasar Lebanon a shekara ta 2000, kamar yadda kuma shakku kan irin martanin da kungiyar za ta mayar ne, ke hana Isra’ila aiwatar da duk wani kudirinta na mamaye wasu yankuna a kasar Lebanon.
3922046