IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Bukaci A Hukunta Masu Keta Alfarmar Kur’ani

14:44 - September 16, 2020
Lambar Labari: 3485189
Tehran (IQNA) kungiyar kasashen musulmi ta bukaci a dauki kwakkwaran mataki na hukunta masu keta alfarmar kur’ani mai tsarki.

Jakadan kasar Pakistan a majalisar dinkin duniya Khalil Hashimi a yayin da yake halartar zaman kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duiya a birnin Grneva na kasar Austria ya bayyana cewa, keta alfarmar kur’ani mai tsarki da wasu masu kiyayya da musulunci suke yia  kasashen turai ba abu ne da za a amince da shi ba.

Jakadan na kasar Pakistan wanda yake wakiltar kungiyar kasashen musulmi a taron ya bayyana cewa, keta alfarmar kur’ani ko cin zarafi manzo ba za su taba zama bangaren na fadin albarkacin baki  ko bayyana ra’ayi ba, domin kuwa wannan batu na akida ta addinin musulunci.

Ya ce kungiyar kasashen msuulmi tana yin kira ga gwamnatocin da aka kona kur’ani mai tsarki a cikin kasashensu, da su gagaguta daukar matakin kame dukkanin wadanda suke da hannua  cikin lamarin domin gabatar da su a  kotu domin hukunta su.

3923319

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kwakkwaran mataki hukunta
captcha