IQNA

Iran Ta Bukaci Iraki Ta Bayar Da Kariya Ga Jami’anta Na Diflomasiyya

21:50 - September 18, 2020
Lambar Labari: 3485196
Tehran (IQNA) Gwamnatin Iran ta bukaci gwamnatin kasar Iraki da ta bayar da kariya ga jami’anta na diflomasiyya da ke Bagadaza da sauran yankunan kasar.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Saeed Khatib Zadeh ne ya yi wannan kira, inda ya bayyana cewa kare jami’an diflomasiyya da kuma wurare na diflomasiyya abu ne da ya zama wajibi a kan kowace kasa.

Ya ce harin da wasu suka kaiwa jami’an huldar diflomasiyyar Iran a cikin birnin Bagadaza abin Allawadai ne, a kan haka suna kira ga gwamnatin kasar Iraki da ta dauki tsauraran matakai na bayar da kariya ga jami’an na Iran da kuma sauran wurarenta na diflomasiyya da ke cikin Iraki.

A jiya ne wasu ‘yan bindiga suka kaiwa ayarin motocin jami’an huldar diflomasiyya na Iran hari a cikin birnin Bagadaza, amma babu wani wanda ya rasa ransa ko jikkata, yayin da ‘yan bindigar suka ranta cikin na kare.

3923586

 

 

 

captcha