Mai magana da yawun kungiyar Ansarullah a kasar Yemen ya ce larabawan da suka kulla alaka da Isra’ila, ba za su iya canja mumummunan tarihin Isra'ila ba.
Tashar Almasirah ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayanin da ya fitar a jiya, Kakakin kungiyar Ansarullah da aka fi da kungiyar Alhuthi, Muhammad Abdulsalam ya bayyana cewa, larabawan da suka kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila, ba za su iya goge bakin fentin da ke a fuskar Isra’ila ba, kuma ba za su iya samar mata da halasci ba, domin kuwa ta ginu ne a kan haramci ta hanyar mamayar kasar Falastinawa tare da zubar da jininsu.
Ya ce dukkanin kasashen larabawan da suka kulla alaka da Isra’ila, dama can ‘yan amshin shata ne na Amurka da yahudawa, kuma abin takaici a nan shi ne, an ba su umarnin yin hakan ne, su kuma suka aiwatar a cikin kaskanci, domin kuwa ba da yawun al’ummomin kasashensu suka yi haka ba.
Ya kara da cewa, abin da ya faru ya yi kama da izgili ko kuma wasan kwaikwayo, domin kuwa kasashen da suke da tsohowar alaka ta boye tare da yahudawan Isra’ila, kuma ba su da wata matsala da Isra’ila ba, kamar yadda ma ba a taba jin sun yi ko da Allawadai ne da kisan kiyashin da Isra’ila take yi kan Falastinawa ba, wadannan kasashen ne kuma a yau suke cewa sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya tare da Isra’ila.
3923554