IQNA

Jagoran Juyin Musulunci Na Iran:
23:27 - September 21, 2020
Lambar Labari: 3485204
Tehran (IQNA) Ayatollah Khamenei jagoran juyin a Iran ya bayyana kalafaffen yaki a kan Iran da cewa  yana a matsayin kariyar kai wanda musulunci ya yi umarni da shi.

Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya bayyana yakin da aka kallafa ma kasar har tsawon shekaru 8, yana a matsayin kariyar kai wanda musulunci ya yi umarni da shi kuma yake a matsayin wajibi.

A lokacin da yake gabatar da jawabin nasa ayau, wanda dukkanin kafofin yada labarai na kasar Iran suka watsa kai tsaye, jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, kasar Iran ta kare kanta tsawon shekaru 8 a jere a yakin da aka kallafa mata.

Ya ce duk da cewa a lokacin ba ajima da saumun nasarar juyi a kasar ba, amma duk da haka sakamakon dogaro da Allah da kuma mika lamari a gare shi, kasar ta samu nasara a kan manyan kasashen duniya wadanda su ne suka yi yakin a kan Iran ba Saddam Hussain ba, wanda shi ya kasace wanda suke yin amfani da shi ne kawai a yakin.

Jagoran ya kara da cewa, gogewar da al’ummar kasar suka samu a wannan lokaci, ita ce ta ba su damar samun dukkanin ci gaban da suke da shi a halin yanzu, ta fuskacin kere-kere da kuma ci gaban ilimi da sauran bangarori na rayuwa.

 

3924250

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: