IQNA

‘Yan Saudiyya Sun Kafa Jam’iyyar Siyasa Domin Kafa Dimukradiyya A Kasar

22:19 - September 24, 2020
Lambar Labari: 3485214
‘Yan Saudiyya mazauna kasashen waje sun sanar da kafa jam’iyyar siyasa domin kafa tsarin demokradiyyar a kasar mai maon mulkin mulukiya da kama karya.

Fitattun ‘yan kasar ta Saudiyya ne mazauna kasashen waje su ka sanar da kafa jam’iyyar siyasa domin kafa tsarin demokradiyyar a Saudiyyar da su ka bai wa sunan; “Tafarkin Kasa”

Bayanin kafa jam’iyyar ya kunshi cewa; Manufarsa shi ne kare kasar daga fadawa cikin rikice-rikice da kuma karfafa alakarta da kasashen duniya da kuma yanki, ta yadda za a kare manufofin al’ummar kasar.

Bugu da kari, bayanin ya yi kira da a yi zaben ‘yan majalisar wakilai a Saudiyyar da kuma raba banagrorin gwamnati uku da juna, bisa yadda ya dace da tsarin mulki.

Daga cikin wadanda su ka kafa sabuwar jam’iyyar ta Saudiyya da akwai, Midhawi Rashid, wacce malamar jami’a ce a Birtaniya, wacce ta fadawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa; Lokacin da aka zaba na kafa jam’iyyar yana da muhimmanci, domin ana kara takurawa ‘yan kasa.”

Sai kuma Yahya Asiry, wanda shi ne shugaban kungiyar ‘al-qisdh’ ta kare hakkin dan’adam da kuma dan shehun malamin nan da yake tsare a Saudiyya, wato Abdullahi Audah. Sai kuma Sa’id Nasir al-Gamidy da kuma Ahmad al-mushaikhis.

3925045

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: fadawa cikin
captcha