IQNA

Bashar Assad: Babu Batun Kulla Alaka Tsakanin Syria Da Isra’ila

22:26 - October 08, 2020
Lambar Labari: 3485259
Shugaban kasar Syria Bashar Assad ya mayar da martani kan shirin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi ne neman yi masa kisan gilla.

Tehran (IQNA) shugaban kasar Syria Bashar Assad ya ce babu batun kulla alaka tsakanin Syria da yahudawan Isra’ila.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran sputnik na kasar Rasha, shugaba Assad a lokacin da yake amsa tambaya kan batun yiwuwar kulla alaka tsakanin kasar Syria da gwamnatin yahudawan Isra’ila kuwa, ya ce babu batun kulla alaka tsakanin Syria da yahudawan Isra’ila, matukar dai suna ci gaba da mamaye wasu yankunan na Syria da Falastinu.

Haka nan kuma ya bayyana furucin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na neman yin kisan gilla a kansa da cewa, ya kara fito da siyasar Amurka fili kan cewa siyasa ce ta ‘yan daba da ina da kisa.

Assad ya ce wannan tsari na siyasar Amurka, wanda kuma ba zai kawo karshe ba har sai ranar da aka kawo karshen tsarin dabanci da ina da kisa da haifar da fitintinua cikin kasashen duniya, da haifar da yake-yake tsakanin al’ummomi da rarraba kawunansu domin mallake arzikinsu, da dai sauran halaye wadanda siyasar Amurka ta ginu a kansu.

Shugaba Assad ya ce Amurka ta saka kafarta a cikin kasar Syria da sunan yaki da ta’addanci, amma bababr manufar hakan ba yaki da ta’addanci ba, manufar ita ce karfafa ta’addanci domin ganin bayan gwamnatin Syria.

Ya kara da cewa idan Amurka ta ci gaba da kasancewa cikin kasar Syria, to lokaci zai zo wanda al’ummar kasar ne da kansu za su fitar da ita da karfi, ta hanyar yi mata da kuma tilasta ta ficewa.

 

 

3928102

 

 

 

captcha