IQNA

An Kama Mutane Da Dama Sakamakon Halartar Tarukan Arba’in A Bahrain

23:56 - October 12, 2020
Lambar Labari: 3485270
Tehran (IQNA) masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain ta kama adadi mai yawa na mutanen kasar da suka halarci tarukan juyayin arba’in a cikin wannan mako.

Rahotanni daga kasar Bahrain sun ce masarautar mulkin mulukiyya da kama karya ta kasar ta kama adadi mai yawa na mutanen kasar da suka halarci tarukann juyayin arba’in na Imam Hussain (AS) da aka gudanar a sassa na kasar.

Babbar jam’iyyar siyasa ta kasar Bahrain Alwifaq ta sanar da cewa, jami’an tsaron masarautar kasar suna bi gida-gida suna kama mutane bisa zargin su da halartar tarukan arba’in na Imam Hussain (AS) a wannan shekara.

Daga cikin wadanda aka kama baya ga sauran jama’ar gari, an kuma kama wasu  daga malamai da suka gabatar da jawabai a wuraren tarukan.

Tun daruwan shekaru da suka gabata al’ummar kasar Bahrain wadanda akasarinsu mabiya mazhabar shi’a ne, suna gudanar da irin wadannan taruka, amma masarautar kasar da ke mulki a halin wadda turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka kafa, tana daukar matakan takurawa a kansu.

 

3928897

 

 

captcha