IQNA

‘Yan Sandan Jamus Sun Keta Alfarmar Masallaci A Birnin Berlin

22:41 - October 22, 2020
Lambar Labari: 3485297
Tehran (IQNA) jami’an ‘yan sandan kasar Jamus sun keta alfarmar wani masallaci a cikin birnin Berlin.

Jaridar Quds Alrabi ta bayar da rahoton cewa, a jiya jami’an ‘yan sandan gwamnatin kasar Jamus sun keta alfarmar wani masallaci a cikin birnin Berlin ta hanyar kutsa kai a cikinsa da takalma a kafafunsu.

Rahoton ya ce ‘yan sanda sun kai samame ne a masallacin Maulana da ke birnin na Berlin, inda kimanin ‘yan sanda 150 sanye da kayan sarki suka kutsa kai cikin masallacin, tare da keta akfarmarsa.

‘Yan sandan sun kai wannan samame ne bisa hujjar cewa kotu ta bayar da umarnin bincika masallatai 5, saboda tara kudade da suke yi domin taimakawa masu dauke da cutar corona, wanda hakan ya sabawa doka.

Babban limamin masallacin Idrs Qahriman ya bayyana cewa, kafin ‘yan sanda su shiga cikin masallacin, sun fara zuwa gidansa ne inda suka yi bincike.

Wannan dai na daya daga cikin matakan hukumomi a kasashen turai suke dauka na nuna kyama ga musulmi da addinin muslunci a cikin ‘yan kwanakin nan.

 

3930724

 

 

 

captcha