IQNA

Iran Ta Sanar Da Kakaba Wa Wasu Jami’an Gwamnatin Amurka Takunkumi

23:33 - October 23, 2020
Lambar Labari: 3485300
Tehran (IQNA) ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta sanar da kakaba wa wasu jami’an gwamnatin Amurka takunkumi.

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib Zadeh ya fitar, ya sanar da cewa sakamakon daukar nauyin ayyukan ta’addanci da take hakkokin bil adam da aka samu wasu jami’an huldar diflomasiyyar Amurka da hannu a cikinsu, Iran ta kakaba wa wasu daga cikinsu takunkumi.

Ya ce wannan takunkumi ya hada da jakadan Amurka a Iraki da kuma mataimakinsa, gami da shugaban karamin ofishin jakadancin Amurka da ke Arbil a yankin Kurdestan a Iraki.

Bayanin ya ce dukkanin wadannan mutane suna da hannu a ayyukan ta’addanci daban-daban a yankin gabas ta tsakiya, daga ciki kuwa har da kisan babban jami’in soja na kasar Iran janar Qaasem Sulamani.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, jami’an huldar diflomasiyyar Amurka a Iraki suna da hannu wajen taimaka ma kungiyoyin ta’addanci irin su Daesh alkaida da makamantansu a dukkanin ayyukan ta’addancin da suka aikata kan al’ummar Iraki da ma yankin gabas ta tsakiya.

 

3930882

 

 

captcha