IQNA

Al’ummar Kuwait Sun Kaurace Wa Sayen Kayan Faransa Saboda Cin Zarafin Ma’aiki

23:24 - October 26, 2020
Lambar Labari: 3485308
Tehran (IQNA) sanadiyyar yin batunci ga manzon Allah a Faransa an kaurace wa sayen kayayyakin kasar ta Faransa a Kuwait.

Sakamakon ci gaba da yin batunci ga manzon Allah (SAW) da ake yi a kasar Faransa, jama’a da dama a kasar Kuwait sun kaurace wa sayen kayayyakin kasar ta Faransa.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, ma’aikatar harkokin wajen kasar Kuwait ta fitar da wani bayani, wanda a cikinsa ta nuna bacin rai matuka dangane da yadda wasu jami’an gwamnatin kasar Faransa suka fitoa fili suna sukar addinin muslunci, tare da nuna goyon baya ga cin zarafin annabawan Allah.

Bayanin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Kuwait ya gargadi kasar Faransa kan yin sakaci da irin wannan lamari mai matukar hadari, wanda zai iya mayar da hannun agogo baya a kan dukkanin kokarin da ake yi tsakanin kasashen na hada kan al’ummomi domin samun zaman lafiya da fahimtar juna, da kuma girmama akidar kowa.

A daya bangaren kuma masu fafutuka a kasar Kuwait sun yi kira a shafukan zumunta kan a kaurace wa duk wasu kayayyakin da ake samar da su a kasar Faransa, ko kuma kamfanonin kasar da suke gudanar da ayyuka a cikin kasar ta Kuwait, domin nuna rashin amincewa da cin zarafin manzon Allah (SAW) da ake yia kasar ta Faransa da sunan ‘yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra’ayi, wanda hakan ke samun goyon baya kai tsaye daga gwamnatin kasar.

Baya ga kasar Kuwait, a wasu kasashen larabawa da na musulmi ma an fara gudanar da wannan kira na kaurace wa kayan Faransa, domin nuna fushi kan keta alfarmar addinin muslunci da ake yi a kasar.

 

 

3930933

 

 

 

 

captcha