IQNA

Nasrullah: Imani Da Manzon Allah (SAW) Gishiki Ne Na Addinin Muslunci Taba Shi Taba Addini Ne

22:48 - October 31, 2020
Lambar Labari: 3485326
Tehran (IQNA) Sayyid Hassan Nasaralla ya bayyana cewa laifin da ‘yan ta’adda suka aikata bai da dangantaka da addinin musulunci da koyarwarsa.

Jagoran kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa laifin dangantakada ‘yan ta’adda suka aikata bai da dangantaka da addinin musulunci.

Kafofin yada l;abarai sun nakalto Sayyid Nasarallah yana fadar haka a jiya Jumma’a a lokacinda yake jawabi dangane da maulidin manzon Allah (s).

Sayyid Nasarallah ya kara da cewa musulmi basu dorawa addinin kirista ko annabi Isa (a) laifukan  ta’addanci wanda Amurka da kasashen yamma suka aikata a kasashen Iraki, Siriya da Afganistan.

Shugaban kungiyar ta Hizbullah ya bayyana cewa ‘yancin fadin albarkacin baki a kasashen yamma ba gaskiya bane, don suna nuna fuska biyu a aiwatar da wannan ‘yencin, inda ba’a isa a karyara Holocos ba, wato tastuniyar kissan yahudawa a Jamus.

Amma suka bawa kansu damar cin mutuncin addinin musulunci da musulmi ko manzon addinin musulunci ta yadda suka ga dama, da sunan ‘yanci fadin albarkacin baki.

Daga karshe Sayyid Nasararl ya bukaci kasashen yamma su daika taimakawa yan ta’adda wadanda wadanda suke zubar da jinin mutane ba tare da wani laifi ba.

3932141

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: annabi
captcha