IQNA

22:51 - November 02, 2020
Lambar Labari: 3485328
Tehran (IQNA) shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya aike da sakon taya murnar maulidin manzon Allah (SAW) ga shugabannin kasashen msuulmi na duniya.

Shafin yada labarai an ofishin shugaban kasar Iran ya bayar da bayanin cewa, a  yau shugaba Hassan Rauhani ya aike da sakon taya murnar maulidin manzon Allah (SAW) ga takwarorinsa shugabanni kasashen musulmi na duniya.

Bayanin ya ce,a  cikin sakon shugaba Rauhani ya bayyana zagayowar lokacin haihuwar fiyayyen halitta lokaci ne mai albarka kuam ami matukar muhimamnci ga dukaknin musulmi na duniya, domin kuwa ita ce ranar da aka haifi halitta mafi daraja a tsakanin dukkanin halittun da Allah ya halitta.

Wannan haske da ya zo duniya a wanann rana shi ne rahma ga dukkanin talikai da Allah ya kawo a tsakanin bil adama, shi ne yake dauke da shiryar ubangiji zuwa ga talikai baki daya, saboda haka farin ciki da wannan rana farin ciki ne da ni’imar da Allah ya yi wa duniya da zuwan babban masyinsa.

Haka nan kuam shugaba Rauhani ya bayyana duk nauin aiki na cin zarafi da batunci ga wannan mutum mai daraja da madaukakin matsayi manzon karshe daga cikin annabawan Alalh Muhammad dan Allah (SAW) ba  abu ne da musulmi za su lamunta da shi ba, domin mutuncin manzon Allah da martbarsa suna gaban komai a wajen musulmi.

Daga karshe ya yi fatan Alah ya kawo karshen cutar corona da ta adabi duniya baki daya.

 

3932939

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: