IQNA

23:40 - November 07, 2020
Lambar Labari: 3485343
Tehran (IQNA) a jiya ne Allah ya yi wa sheikh Nurain Muhamma Sadiq fitaccen makarancin kur’ani dan kasar Sudan rasuwa.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Nasruddin Mufrih ministar mai kula da harkokin addini a kasar Sudan ya bayyana cewa, Allah ya yi wa sheikh Nurain Muhamma Sadiq fitaccen makarancin kur’ani dan kasar Sudan rasuwa sakamakon wani hadarin mota.

Wannan hadari dai ya faru ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga wata gayyata da aka yi masa tare da wasu mahardata kur’ani da suke a cikin mota guda, inda baya ga shi, wasu uku sun rasu, wani guda kuma ya samu raunuka.

Mataimakin shugaban majalisar mulki ta kasar Sudan Muhammad Hamdan ya sanar da wannan rasuwa a cikin shafinsa na facebook, inda ya isar da sakon ta’aziyya da kuma juyayin abin da ya faru.

sheikh Nurain Muhamma Sadiq dai faitaccen makaranin kur’ani ne wanda jama’a suke son karatunsa a kasar Sudan da ma wasu kasashen ketare, inda akan ji karatunsa a cikin motoci da wuraren taruwar jama’a da masallataia  kasar Sudan.

Ya fi shahara da salon karatu na tartil, kamar yadda kuma ya halarci tarukan karatun kur’ani a kasashen duniya da dama, ya kuma karbi kyautuka na kasa da kasa a fannin karatun kur’ani mai tsarki.

3933601

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: