IQNA

14:49 - November 12, 2020
Lambar Labari: 3485360
Tehran (IQNA) Mataimakiyar zababben shugaban Amurka mai jiran gado Kamala Harris ta ce za su dawo da alaka tsakanin Amurka da kuma gwamnatin Falastinawa.

A cikin wani rahoto da tashar alalam ta bayar ta bayyana cewa, Kamala Harris mataimakiyar zababben shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden ta ce, idan suka karbi mulki za su sake dawo da alaka tsakanin Amurka da kuma gwamnatin Falastinawa, wadda Donald Trump ya rusa.

Kamala Harris ta ce, dukkanin ofisoshin gwamnatin kwarya-kwaryan cin gishin kai ta Falastinawa da ke Amurka wadanda Trump ya rufe, za a sake bude domin su gaba da aiki.

Dangane da taimakon da Amurak take baiwa Falastinawa kuwa wanda Trump ya yanke, Harris ta ce za su ci gaba da baiwa Falastinawa taimakon da Amurka ke ba su, kamar yadda kuma a yankin zirin Gaza ma Amurka za ta maido da ayyukanta na jin kai.

 

3934755

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: