Ministan tsaron kasar Iraki Juma’a Inad Sa’adun ne ya bayyana hakan a yau a lokacin da yake ganawa da babban hafsan hafsoshin soji na kasar Iran janar Muhammad Baqiri a birnin Tehran.
A yayin da yake tarbar ministan tsaron kasar Iraki a yau, babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran janar Baqiri ya bayyana cewa, kasahen biyu sun himmatu matuka wajen karfafa dangantakarsu ta tsaro, sakamakon barazanar da suke fuskanta.
Ya ce babu wani abu shamaki a lakar Iran da Iraki a dukkanin bangarori, da hakan ya hada har da bangaren tsaro, wanda sun yi nisa wajen fadada ayyukansu na hadin gwiwa a wannan fage.
Shi ma a nasa bangaren ministan tsaron kasar Iraki Inda Sa’adun ya jaddada cewa, babu gudu babu ja da baya wajen ci gab ada gudanar da ayyukan tsaro na hadin gwiwa adukkanin bangarori tsakanin Iran da Iraki, kuma Iraki ba ta shayin kowa dangane da shirinta na sayen makamai daga kasar Iran.
Ziyarar ministan tsaron kasar Irakia Iran dai na zuwa ne ‘yn makonni bayan dauke wa Iran takunkumin saye da sayar da makamai.