IQNA

22:47 - November 16, 2020
Lambar Labari: 3485371
Tehran (IQNA) kafofin yada labaran Syria sun sanar da rasuwar ministan harkokin wajen kasar da safiyar yau Litinin yana da shekaru saba'in da tara.

Shi dai Walid al-mu’allim an haife shi ne a 1941 a birnin Damascuss na kasar ta Syria kuma ya yi karatukansa ne a cikin kasar da kuma birnin al-kahira na kasar Masar.

Bayan da ya fara aiki da ma’aikatar harkokin wajen kasar a 1964, ya yi ayyukan diplomasiyya a kasashen Tanzania, Saudiyya, Spain da kuma Birtania

Daga cikin kasashen da ya yi wa kasarsa jakadanci da akwai Romania da kuma Amurka, sannan ya zama mataimakin ministan harkokin waje daga 2000, yayin da ya zama minstan harkokin waje a 2006.

Baya ga aiki diplomasiyyar da ya yi, Walid Mu’allim ya bar littatafai da ya rubuta akan palasdinu, Syria a karkashin mulkin mallaka da kuma bayan samun ‘yancin kasar sannan kuma gabas ta tsakiya da yadda Amurka take daukarsa.

3935452

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Amurka ، Palastinu ، safiyar ، Litinin ، Walid al-mu’allim
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: