IQNA

22:56 - November 17, 2020
Lambar Labari: 3485376
Gwamnatin kasar Amurka ta samar da wani tsari na leken asiri a kan musulmin kasar ta hanyar wayoyin salula.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, kungiyar kare hakkokin musulmi ta kasar Amurka CAIR ta bayar da bayanin cewa, a halin yanzu hukumomin leken asiri na Amurka samar da wani tsari na leken asiri a kan musulmin kasar, wanda aka sanya a cikin tsarin manjar da ake saukewa  acikin wayoyin hannu.

Kungiyar ta ce jami’an tsaron Amurka sun yi hakan ne da sunan yaki da ta’addanci, inda suke yin leken asiri a kan musulmin kasar bisa zarginsu da dangantaka da ‘yan ta’adda, tare da sauraren dukkanin zantukansu ta hanyar wayoyinsu.

Bayanin ya ce wannan take hakkokin musulmi ne, domin kuwa babu wani dalili da zai sanya a dora alamar tambaya a kan kowane musulmi bisa zarginsa da alaka da ‘yan ta’adda saboda kawai yana musulmi.

Tun kafin wannan lokacin dai musulmin kasar Amurka suna kokawa kan yada ake bin diddigin lamurransu, ta yadda ba su da sirri a tsakaninsu da danginsu da iyalansu da ma sauran abokan harkokinsu na yau da kullum.

 

3935787

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: