IQNA

Dan Wasan Arsenal Ya Yi Kira Da A Kawo Karshen Nuna Wa Musulmi Kyama A Turai

23:50 - November 21, 2020
Lambar Labari: 3485387
Tehran (IQNA) Masud Ozil dan wasan kwallon kafa musulmi na kungiyar Arsenal ya yi kira da a kawo karshen nuna kiyayya da ake yi musulmi a  turai.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya bayar da rahoton cewa, Masud Ozil dan wasan kwallon kafa musulmi da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a Burtaniya, ya bayyana yadda ake samun karuwar kin jinin musulmi musamman a kasashen turai da cewa abin takaici ne.

Ya ce yana da kyau ga gwamnatoci su mike domin tunkarar wannan matsala mai matukar hatsari a cikin kasashensu, domin hakan yana da mummunan tasiri a cikin rayuwar zamantakewa ta al’umma.

Dangane da su kuma musulmi kuwa musamman wadanda suke rayuwa a cikin wadannan kasashe, ya ce ya zama wajibi su fuskanci lamarin ta hanyar da ta dace, wato nuna kyawawan dabiu irin na addinin musulunci, ba ta hanyar yin abin da zai iya kara bata sunan addinin musulunci ba.

Ya yi ishara da aya ta 34 a cikin surat Fusilat a cikin kur’ani mai tsarki, da ke yin ishara da cewa abu mai kyau da maras kyau ba za taba zama daya ba.

Ozil dan asalin kasar Turkiya wanda yake da shedar zama dan kasa a Jamus, ya bayyana cewa a duk lokacin da ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Jamus wasa kuma aka samu nasara, a lokacin ‘yan kasar sukan kira shi da dan kasar Jamus, amma idan ba a yi nasara ba, su kan kira shi da bakon haure, inda a cewarsa wannan duk nau’i ne na irin na wariyar da ake nuna wa musulmi a turai. 

 

3936300

 

captcha