Jagoran juyin juya halin mulsunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da sako a yau dangane da kisan da aka yi wa babban masanin ilimin nukiliya na kasar Iran Mohsen Fakhrizadeh.
Matanin Sakon Jagora:
Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Kai
Fitaccen masani kan harkokin na ilimin nukiliya da kuma tsaro Malam Mohsen Fakhrizadeh ya yi shahada a hannun ‘yan kwangila masu kekasassar zuciya.
Hakika shi mutum ne da ya kasance mai kokari matuka, da himma maras tamka a cikin rayuwarsa, domin ganin ya yi hidima ga addinin Allah da kuma bayanin Allah, saboda haka yin shahada da ya yi wata babbar kyauta ce ya samu daga Allah.
Akwai abubuwa guda biyu da ya zama wajibi a mayar da hankalia kansu bayan kisan gillar da aka yi masa, na daya a bi diddigin lamarin domin gano dukkanin wadanda suke da hannu a kisansa, da kuma wadanda suka sanya su, kuma a dauki matakin da ya dace a kansu.
Na biyu kuma a ci gaba da kara bunkasa ayyuka na ilimi a fagen da yake yake bayar da gudunmawa, a bangaren nukiliya da sauran bangarori na tsaron kasa.
Daga karshe ina mika sakon ta’aziyya ga iyalansa, da kuma sauran abokan aikinsa a dukkanin bangarori.
Sayyid Ali Khamenei
28/11/2020