Shafin yada labarai an News Vision ya bayar da rahoton cewa, musulmin yankin Zigoti na kasar Uganda, sun sanar da cewa, za su gina wata cibiyar kur’ani da kuma asibitia cikin farfajiyar wani babban masallaci a yankin.
Ali Kitza wanda shi ne jagoran musulmi a kasar Uganda ya bayyana cewa, wannan masallaci yana daga cikin amnyan masallatai na kasar, kuma ginin wannan babbar cibiya ta kur’ani yana daga cikin ayyukan masu matukar muhimamnci da musulmin kasar suka sanya a gaba.
Baya ga haka kuma ya bayyana cewa, za a gina asibiti wadda za ta kiyaye kaidoji na muslunci, wadda kuma dukkanin mutane musulmi da wadanda ba musulmi za su iya mafana da wannan asibiti domin samun lafiya.
Haji Nu’uman Natamba, daya daga cikin jagororin musulmi a kasar Uganda ya bayyana cewa, da yardarm Allah wannan aiki zai kammala nan bad a jimawa ba, domin kuwa musulmin kasar ne baki daya suke bayar ad dukkanin taimakonsu domin ganin an kammala aikin.