IQNA

Taron Cibiyar Musulmi Ta Burtaniya Kan Karuwar Kyamar Musulmi

22:46 - December 01, 2020
Lambar Labari: 3485419
Tehran (IQNA) babbar cibiyar musulmi a  Burtaniya za ta gudanar da taron karawa juna sani na shekara-shekara wanda zai yi dubi kan kyamar musulmi.

Cibiyar musulmin tare ad hadi gwiwa da kungiyar nan mai fada da manufofin mulkin mallaka ta Decolonial International Network ne za su gudanar da taron na wannan shekara, wanda shi ne karo na bakwai da ake gudanarwa.

Cibiyar ta yi bayania  cikin shafinta na yanar gizo kan cewa, a cikin shekara ta 2011, gwamnatin Burtaniya ta fitar da wani tsari na gudanar da bincike a kan musulmi bisa zarginsu da ta’addanci, wanda akan hakan an cutar da musulmi da dama ba su san hawa ba balanta sauka.

A kasar Faransa ma a cikin shekarun baya-bayan nan an fara aiwatar da wani shiri makamancin hakan, inda aka sanya ido a kan musulmitare da bibiyar lamarinsu, har ma da yi masu tambayoyi na kwakwaf duk bisa danganta su da ayyukan ta’addanci.

Ita ma anata bangaren gwamnatin kasar Austria ta bi sahun irin wadanna kasashe, wajen kirkiro sabbin dokoki na takura musulmi mazauna kasar, wanda hakan ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na duniya, bil hasali ma take hakkokin bil adama ne, domin musulmi ‘yan adam kamar kowa a duniya.

A kan haka taron zai bahasi tare da jin mahangar masana a kan wannan batu ta fuskoki daban-daban, na siyasa, zamantakewa da kuma doka.

Taron dai zai gudana ne a ranar 13 ga wannan wata na Disamba tare da gabatar da bayanai daga masana daga sassa na duniya.

 

3938614

 

captcha