Shafin yada labarai na Algad ya bayar da rahoton cewa, wasu gungun matasan yahudawa dake samun kariya daga jami’an tsaron Isra’ila sun auka cikin masallacin Quds mai alfarma, tare da keta alfarmar wurin mai tsarki.
Baya ga haka kuma wasu gungun daruruwan yahudawan das u ma suke samun kariya daga jami’an tsaron Ira’ila, sun auka a cikin masallacin annabi Ibrahim (AS) da ke garin Alkhalil, tare da keta alfarmar masallacin.
A nata bangaren gwamnatin Falastinawa ta yi gargadi dangane da irin wadannan matakai na tsokana da yahudawan Isra’ila suke dauka a kan wurare masu tsarki na musulmi da ke cikin Falastinu.
Bayanin gwamnatin Falastinawa ya ce, irin wannan mummunan aiki da yahudawan ke yi a halin yanzu ya zama kusan a kowane lokaci, inda sukan shiga cikin masallatai musamman masallacin quds da masallacin annabi Ibrahim da takalmansu.
A shekarun baya yahudawan sukan shiga wadannan wuraren ne a wasu ranaku na musamman a shekara da suke girmamawa, da kuma suke danganta wadannan wurare da ranakun, amma a yanzu duk lokacin da suka ga dama za su kutsa kai.