IQNA

22:11 - December 03, 2020
Lambar Labari: 3485424
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Faransa za ta rufe wasu masallatai da sunan sanya ido a kan musulmi domin yaki da tsatsauran ra’ayi.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Faransa ya sanar da cewa, nan da ‘yan kwanaki masu zuwa gwamnatin kasar za ta rufe masallatai kimanin 76 a kasar, domin yaki da abin da ya kira tsatsauran ra’ayi.

Bayanin ya ce wuraren za a rika sanya idanu ne a kansu da kuma gudanar da bincike, domin tabbatar da cewa babu wani abu da ake yi wanda ya saba wa doka, kuma wuraren sun hada da masallatai da cibiyoyin taruka na addini.

Daga cikin wuraren akwai masallatai kimanin 16 a cikin birnin Paris, sa kuma sauran kimanin 60 daga cikinsu a sauran wurare da ke cikin fadin kasar.

Bayanin ministan ya ce akwai yiwuwar za a rufe wasu daga cikin wadannan masallatai da cibiyoyi na musulmi, sakamakon yadda ake yin amfani da su wajen watsa tsatsauran ra’ayi, wanda kuma hakan yana a matsayin barazana ga harkar tsaro.

Dukkanin wadannan matakai za su shafi musulmi ne kawai, ba za su shafi bangaren wasu addinai ba.

Wannan dai yana daga cikin irin matakan da gwamnatin Macron take dauka na shiga kafar wando daya da musulmi da suna yaki da ta’addanci, inda daga lokacin da ya karbi shugabancin kasar ya zuwa yanzu ya rufe masallatai 43 a fadin kasar.

3938896

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: