IQNA

Mataimakin Kungiyar Ahdullah Ta Iraki A Zantawa Da IQNA:

Amurka Da Isra’ila Ne Ke Da Hannu A Kisan Babban Masanin Nukiliya Na Kasar Iran

22:26 - December 06, 2020
Lambar Labari: 3485433
Tehran (IQNA) Masani kan harkokin siyasar kasa da kasa daga kasar Iraki ya sheda wa kamfanin dillancin labaran iqna cewa, tabbas Amurka da Isra’ila ne suka kashe Fakhrizadeh.

Juma’a Alatwani mamba a kungiyar Ahdullah a kasar Iraki kuma masani kan harkokin siyasar kasa da kasa daga kasar Iraki ya sheda wa kamfanin dillancin labaran iqna cewa, tabbas Amurka da Isra’ila ne suka kashe Fakhrizadeh da sauran masanan kasar da aka yi wa kisan gilla a baya.

Ya ce irin wannan mataki yana nuni da yadda Amurka da Isra’ila suke kallon tasirin kasar ta Iran a dukkanin bangarori a yankin gabas ta tsakiya, kuma suna kallon kasar a matsayin babbar barazana da za ta iya zama babban karfe kafa ga manufofinsu na siyasar mulkin mallaka da mamaye arzikin al’ummomin kasashen yankin.

Ko shakka babu kisan Mohsen Fakhrizadeh ya zo ne a daidai lokacin da Amurka da Isra’ila da kuma ‘yan korensu a yankin da suke yi musu amshin shata daga cikin kasashen larabawa masu tsananin kiyayya da Iran, suke son daukar fansa a kan kasar, sakamakon gagarumin ci gaban da ta samu a cikin kankanin lokaci a bangarori daban-daban na ilimi, da hakan ya hada har da bangaren nukiliya.

Tabbas Martanin Iran Zai Zama Mai Girgizawa

Masanin na kasar Iraki ya ce, tabbas Iran za ta mayar da martani kan wannan babban laifi na ta’addanci, kuma martanin zai zama mai girgizawa ne matuka ga masu hannu a cikin lamarin. Ya ce kasantuwar kasar ta Iran tana da masaniya  akan irin wadannan lamurra, ta san hanyoyin da zata bi domin mayar da martanin da ya dace.

Dangane da yadda majalisar dinkin duniya ta mayar da martani kan lamarin kuwa, ya bayyana cewa abin kunya ne, domin kuwa laifi na ta’addanci da aka aikata  a cikin kasa mai ‘yanci kuma cikakkiyar mamba a wannan majalisa, amma sai majalisar ta takaita da yin Allawadai kawai, maimakon yin kira da a gudanar  da dabincike domin gano masu laifin domin su fuskanci hukunci, kamar yadda take yi idan irin wannan ta faru a kan wasu kasashen.

 

3938127

 

 

captcha