A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna, farfesa Phillis Steven Jr ya bayyana cewa, wasu da dama suna tunanin za a samu gagarumin sauyi a cikin lamurra da zaran an kammala karbar mulki daga hannun Donald Trump.
Ya ce wannan ba abu ne mai sauki ba, domin kuwa tabbas za a ci gaba da ganin ayyukan dabanci da ke cikin siyasar Trump a cikin lamurra na zamantakewar al’ummomin Amurka, domin kuwa akwai mutanen da sun tasirantu da irin wannan salon siyasa tasa.
Dangane da yadda yake kallon sauyin da za a iya samu kuwa, ya bayyana cewa, zai iya zama tafuskar siyasar Amurka a wajen kasar ne, wato yadda siyasar Amurka take dangane da kasashen duniya, a bayan Trump za a iya samun gagarumin sauyi ta wannan fuska.
Amma dangane da masu tunanin bangaranci da nuna wariyar launin fata ko ta addini wadda Trump ya assasa, za a ci gaba da ganin halayya irin wannan lokaci zuwa a cikin yankunan kasar Amurka har na da shekaru masu zuwa.
3939609