A yau ne aka kammala taron gasar kur'ani ta kasa baki daya a kasar Iran, tare da halartar Ministan al'adu Sayyid Abbas Salehi, Sayyid Mahdi Khamushi shugaban hukumar kula da harkokin addini ta kasa gami da wasu manyan jami'ai, an gudanar da taron ne a dakin taro na otel din Eram a birnin Tehran.