Shafin yada labarai na Misr Yaum ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar Mauritania ta bullo da shirin karatun kur’ani domin rokon Allah ya kawo karshen cutar corona, wanda za a rika gudanarwa a wurare daban-daban.
Baya ga haka kuma za a rika saka karatun kur’ani a cibiyoyi na addini da masallatai a lokuta daban-daban, domin samun albarkar kur’ani mai tsarki wajen kawo karshen wannan annoba da ta addabi duniya.
Minista mai kula da harkoki addini na kasar Mauritania ya sanar da cewa, za a fara wannan shiri daga yau, kuma dukkanin limamai na kasar an sanar das u dangane wannan shiri.
Baya ga haka kuma gwamnatin Mauritania ta bukaci a ci gaba da kara kiyaye ka’idoji da dokoki na kiwon lafiya da jami’an kiwon lafiya suke fada domin kaucewa kamuwa da wannan cuta.