IQNA

Kotun Tarayyar Turai Ta Tabbatar Da Hukuncin Hana Yanka Dabbobi Kafin Sumar Da Su

23:18 - December 18, 2020
Lambar Labari: 3485470
Tehran (IQNA) kotun kasar Belgium ta fitar da hukuncin hana yanka dabbobi kafin sumar da su.

Tashar euro News ta bayar da rahoton cewa, kotun kasar Belgium ta fitar da hukuncin hana yanka dabbobi kafin sumar da su, wanda hakan ke nufin tsarin yanka a cikin addinin musuluni da kuma addinin yahudawa.

A ranar 7 ga watan Yunin 2017 kotun yankin Flemish Region da ke kasar Belgium ta fara yanke wannan hukunci, an kuma fara aiwatar da shi a cikin shekarar 2019.

Wasu masu rajin kare hakkokin dabbobi ne suka shigar da kara, inda suke kalubalantar yadda ake yanka dabbobi da ransu a cikin hayyacinsu, wanda cewarsu hakan ya saba wa dukkanin ka’idoji da dokoki na kare hakkin dabbobi.

Kungiyoyin kare hakkokin dabbobin sun bukaci da a rika somar da dabbobi ta hanyar yi musu allura kafin yanka, inda kuma babbar kotun kasar ta sanya hakan ya zama doka

A nasu bangaren kungiyoyin musulmi da kuma wasu kungiyoyin yahudawa  akasar at Belgium sun kalubalanci wannan hukunci, tare da bayyana shi da cewa ya sabawa a bin da yake rubuce a cikin addinansu dangane da yankan dabbobi.

Wannan ya sanya kotun kundin tsarin mulki ta kasar Belgium ta bukaci kotun kungiyar tarayyar turai da ta yi dubi kan hukuncin, kan ko ya yi daidai da kundin tsarin dokoki na kungiyar tarayyar turai, inda kotun ta tabbatar da cewa ya yi daidai da dokokin tarayyar turai, amma kuma kowace kasa tana ikon ta yi aiki da dokar, ko kuma ta yi mata kwsakwarima daidai da abin da ya dace da maslaharta.

 

3941724

 

 

 

captcha