Shafin yada labarai na PDN ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani jawabi da ya gabatar a daren jiya, Kakakin kungiyar Hamas Fauzi Barhum ya bayyana cewa, mabiya addinin kirista abokan zama ga dukkanin musulmi da suke Falastinu.
Barhum ya bayyana hakan ne a wurin taron da aka saba gudanarwa a kowace shekara na taya mabiya addinin kirista murnar tarukan zagayowar lokacin haihuwar annabi Isa (AS) inda musulmi kan yi musu kara, kamar yadda su ma suke halartar tarukan musulmi a lokutan idi.
Kakakin na Hamas ya ce alaka tsakanin mabiya addinin kirista da musulmi a Falastinu ta tarihi ce, wadda kuma za ta ci gaba da kasancewa a haka.
Ya ce musulmi da kirista suna da makiyi guda daya ne, shi ne makiya Falastinu da suka mamaye wurare masu tsarki na msuulmi da kirista da suke cikin wannan kasa, kamar yadda kuma kiristoci ba a bar su a baya ba wajen fada mamayar yahudawan sahyuniya a dukkanin fagage a cikin fadin Falastinu.