IQNA

23:54 - December 22, 2020
Lambar Labari: 3485483
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da dakatar da dukkanin harkokin shige da fice a kasar sakamakon bullar sabuwar cutar corona.

Gwamnatin kasar ta Saudiyya dai ta sanar da cewa, matakin dakatar da dukkanin harkokin shige da fice a kasar zai shafi dukkanin harkokin zirga-zirga na jiragen sama da suke shiga kasa daga kasashen ketare, kamar yadda jiragen kasar ma ba za su yi tafiya zuwa wata kasa ba.

Haka nan kuma mahukuntan na masarautar Saudiyya sun ce, wannan doka za ta shafi bangaren harkoki na jiragen ruwa da kuma iyakoki na kasa, domin tabbatar da cewa babu shiga babu fita  a kasar.

Sai dai dangane da jirage na kasashen ketare da suke a cikin kasar a lokacin sanar da wannan doka, za su iya ficewa zuwa kasashensu a  duk lokacin da suke bukata.

Saudiyya ta dauki wannan matakin ne bayan da sabuwar cutar corona da ta bulla a kasar Burtaniya, wadda kuma take kara tsanata, tare da fargabar cewa zata iya bazuwa zuwa sauran kasashen duniya.

3942554

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: