IQNA

Darul Kur’an A Kasar Jamus Ta Saka Ayoyin Da Ke Magana Kan Annabi Isa A Ranar Kirsimati

23:00 - December 26, 2020
Lambar Labari: 3485494
Tehran (IQNA) cibiyar darul kur’an akasar Jamus ta saka ayoyin kur’ani mai tsarki da ke magana kan annabi Isa (AS) a matsayin cewa shi manzon Allah ne a ranar kirsimati.

Cibiyar ta sanya karatun kur’ani mai tsarki da sautin marigayi Mostafa Isma’ila aya ta 171 a cikin surat Nisa da ke cewa:

Yã Mutãnen Littãfi! Kada ku zurfafã a cikin addininku. Kuma kada ku faɗa, ga Allah, fãce gaskiya. Abin da aka sani kawai, Masĩ hu ĩsa ɗan Maryama Manzon Allah ne, kuma kalmarSa, yã jẽfa ta zuwa ga Maryama, kuma rũhi ne daga gare Shi. Sabõda haka, ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma kada ku ce, « Uku » . Ku hanu ( daga faɗin haka ) yã fi zama alhẽri a gare ku. Abin da aka sani kawai, Allah Ubangiji ne Guda. TsarkinSa yã tabbata daga wani abin haifuwa ya kasance a gare Shi! Shĩ ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli.

Darul Kur’an na jamus yana da dangantaka ne da cibiyar Imam Ali (AS) da ke garin Hamburg, kuma cibiyar na yada karatun kur’ani na sauti da sauran ayyuka daban-daban na kur’ani ayyukaa  shafukan yanar gizo.

3943286

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: garin hamburg kasar jamus yanar gizo ayyaka
captcha