IQNA

Manyan Alluna Dauke Da Hotunan Qassem Sulamini A Garin Gaza Da Ke Falastinu

19:52 - December 29, 2020
Lambar Labari: 3485505
Tehran (IQNA) a yau an wayi gari a cikin garin Gaza da ke Falastinu da manyan alluna da suke dauke da hotunan Qassem Sulaimani.

A daidai lokacin da ake cikin kwanakin tunawa da cikar shekara guda da kisan gillar da Amurka ta yi  wa babban kwamandan sojin Iran Janar Qassem Sulamini, a yau an wayi gari a cikin garin Gaza da ke Falastinu da manyan alluna da suke dauke da hotunansa.

Rahoton ya ce wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin Falastinawa daban-daban suke fitar da bayanai kan Qassem Sulamini da kuma irin gudunmawar day a baiwa al’ummar falastinu a bangaren gwagwarmaya domin su kare kansu daga mamayar yahudawa.

A nasa bangaren shugaban kungiyar Hamas Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, janar Qassem Sulaimani ya yi shahada ne a tafarkinsa na kare quds alkiblar musulmi ta farko, kuma Amurka da Isra’ila suna kiyayya da shi ne saboda matsayarsa dangane da Falastinu da kuma kin amincewa da zaluncin Isra’ila a kan al’ummar Falastinu da sauran musulmi.

3944270

 

captcha