Tehran (IQNA) jiragen ruwa 7 na sojojin Bangaladesh suna kwashe musulmi 'yan gudun hijirar Rohingya da suke kasar zuwa wani tsibiri mai nisa.
Sojojin kasar Bangaladesh sun yi amfani da manyan jiragen ruwa wajen kwashe musulmi 'yan gudun hijirar Rohingya 1804 zuwa wani tsibiri mai nisa daga inda aka tsugunnar da su, wanda mutane ba su rayuwa a cikinsa.