IQNA

18:42 - January 14, 2021
Lambar Labari: 3485553
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Canada ta nada wanu musulmi na uku a matsayin minista a kasar.

Shafin yada labarai na jaridar Yeni Shafaq ya bayar da rahoton cewa, a ci gaba da gudanar da sauye-sauyen da firayi ministan kasar Canada Justin Trudeau yake yi a cikin majalisar ministocinsa, ya nada musulmi na uku a matsayin minista.

An nada Umar Algabara dan majalisar dokokin kasar Canada dan asalin kasar Saudiyya, a matsayin sabon ministan sufuri na kasar ta Canada.

Kafin wannan lokacin dai ya kasance mai gudanar da aikace-aikacea  kafofin sada zumunta tsakanin 2006 zuwa 2008, bayanan kuma ya shiga harkokin siyasa, inda aka zabe shi a matsayin dan majalisar dokokin kasar.

Kafin wannan lokacin ma firayi ministan kasar Canada Justin Trudeau ya ayyana wasu ministoci biyu musulmi a  cikin majalisar ministocin kasar, wato Maryam Munsif ‘yar asalin kasar Afghanistan, da kuma Ahmad Hussain dan asalin kasar Somalia.

Maryam Munsif dai mahaifanta sun yi hijira daga kasar Afghanistan zuwa Iran, daga bisani kuma suka nufi kasar Canada a matsayin ‘yan gudun hijira.

 

3947560

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: