IQNA

Trump Ya Bayar Da Babbar Lambar Ban-Girma Ta Amurka Ga Sakin Morocco

23:14 - January 16, 2021
Lambar Labari: 3485560
Tehran (IQNA) Donald Trump ya bayar da babbar lambar ban-girma ta Amurka ga sarkin Moroco saboda kulla hulda da yahudawan Isra’ila.

Shafin yada labarai na Morocco World News ya bayar da rahoton cewa, shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump ya bayar da lambar ban-girma ta Amurka ga sarkin Moroco Muhammad na shida, saboda abin da Trump din ya kira muhimmiyar rawar da ya taka ta fuskar siyasa a gabas ta tsakiya da arewain Afirka.

Fadar White Huse ta ce sarkin na Morocco ya yi rawar gani wajen bunkasa alaka da Amurka, da kuma kokarin ganin an samu daidaito a siyasar gabas ta sakiya, musamman kulla hulda da ya yi da gwamnatin Isra’ila, wanda a cewar bayanin, wannan mataki na jarunta wanda ya cancanci dukkanin yabo.

Jakadiyar kasar Morocco a kasar Amurka  Lalla Joumala ce ta karbi kyautar a madadin sarkin.

Jaridar Sharq Al-ausat ta bayar da rahoton cewa, wasu majiyoyin diflomasiyya na Isra’ila sun tabbatar da cewa, Morocco tana jan kafa wajen bunkasa alakar diflomasiyya da Isra’ila, domin jiran ganin kamun ludden gwamnatin Joe Biden.

Ita ma a nata bangaren jaridar Haaretz ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, har yanzu Morocco ba ta bude ofisoshin diflomasiyya tsakaninta da Isra’ila kamar yadda hadaddiyar daular larabawa da Bahrain suka yi ba, amma dai akwai ofisoshi na tuntuba  a tsakaninsu, sai har yanzu ba a fara wasu manyan ayyuka tsakanin Morocco da Isra’ila ba.

3947979

 

captcha