IQNA

Trump Ya Yi Ikirarin Cewa Zai Sake Dawowa Fadar White House

23:45 - January 20, 2021
Lambar Labari: 3485573
Tehran (IQNA) tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce zai sake dawowa fadar white house.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a wani jawabi da ya yi kafin barin birnin Washington a yau, tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce zai sake dawowa fadar white house a wani lokaci a nan gaba.

A lokacin da yake gabatar da jawabin a gaban wasu magoya bayansa da suka hada da wasu daga cikin jami’an gwamnatinsa, Trump ya bayyana cewa ya samu nasarori masu tarin yawa a cikin shekaru hudu da ya yi yana mulkin Amurka.

Ya ce daga cikin nasarorinsa har da samar da rigakafin cutar corona, bayan nan kuma ya ce a lokacinsa ne aka samu karuwar ma’ikata a kasar, inda ba domin matsalolin corona ba, da an kara samun babban ci gaba a wannan bangare.

Dangane da batun zabe kuwa, ya bayyana cewa ya samu gagarumar nasara, domin kuwa a cewarsa ya samu kuri’u wajen miliyan 75 a zaben da aka gudanar a kasar.

Trump dai ya fice daga fadar white house da jijjifin safiyar yau, bayan fitar da wasu daga cikin kayayyakinsa da aka loda masa a jirgi, ya kuma bar birnin Washington kafin a rantsar da sabon shugaban kasar ta Amurka Joe Biden a yau, inda ya nufi jihar Florida.

 

3948963

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :