IQNA

Jami’an Tsaron Yahudawan Isra’ila Dauke Da Makamai Sun Hana Musulmi Gudanar Da Sallar Juma’a  A Masallacin Quds

22:35 - January 22, 2021
Lambar Labari: 3485577
Tehran (IQNA) jami’an tsaron Isra’ila dauke da muggan makamai sun hana musulmi gudanar da sallar Juma’a a cikin masallacin Quds.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a yau jami’an tsaron Isra’ila dauke da muggan makamai sun hana dubban musulmi gudanar da sallar Juma’a a cikin masallacin Quds.

Umar Alkaswani daraktan cibiyar kula da lamurran masallacin Quds ya bayyana cewa, a duk lokacin da yahudawa suka ga dama suna kutsa kai a cikin masallacin Quds mai alfarma, amma Isra’ila tana hana musulmin yin salla da sunan hana yaduwar corona.

Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin yahudawan Isra’ila ta dauki kwararan matakai na takaita adadin musulmi masu zuwa salla a masallacin Quds, inda ‘yan kalilan ne kawai suke samun izinin yin salla a cikin masallacin mai alfarma.

3949184

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :