IQNA

Bisa Umarnin Kotu Maidakin Sheikh Zakzaky Za Ta Samu Kulawa A Wuraren Killace Masu Dauke Da Corona

22:56 - January 26, 2021
Lambar Labari: 3485592
Tehran (IQNA) bisa umarnin kotu maidakin Sheikh Ibrahim Zakzaky Malama Zeenat Ibrahim za ta samu kulawa a wuraren killace masu dauke da cutar corona.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, bisa gwajin da aka yi wa  maidakin Sheikh Ibrahim Zakzaky Malama Zeenat Ibrahim da ke tabbatar da cewa tana dauke da cutar corona, kotu ta amince da sakamakon gwajin.

Haka nan kuna rahotannin sun ce kotu ta bayar da umarni ga jami’an da ke kula da gidan kason Kaduna, kan a gaggauta daukar matakin kai Malama Zeenat Ibrahim Zakzaky zuwa wurin da ake killace jama’a da suke dauke da cutar ta corona jihar Kaduna.

Dangane da wannan batu na kamuwar malama Zeenat Ibrahim da cutar corona, majiyoyin Harka Islamiyya sun tabbatar da wannan labari, da ke cewa gw2ajin da aka yi mata na wannan cuta ya tabbatar da cewa tana dauke da ita.

Amma masu kula da gidan kason sun nuna rashin amincewarsu da sahihancin sakamakon wannan gwajin, har zuwa lokacin da kotu ta duba sakamakon gwajin kuma ta amince da shi, wanda hakan yasa ala tilas jami'an gidan kason su yi aiki da umarnin kotu.

Tun daga lokacin fitar da wannan sakamakon iyalan Sheikh Zakzaky ne suka fara fitar da wata sanarwa, kan cewa Malama Zenat tana fama da cutar corona a cikin gidan kaso, bayan gwajin da aka yi mata ya tabbatar da hakan, da kuma neman a dauki matakan gaggauwa domin ba ta kula.

 

3949885

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :