IQNA

Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam Na Duniya Sun Fara Kira Da A Duba Gidajen Kason Saudiyya

23:53 - January 29, 2021
Lambar Labari: 3485599
Tehran (IQNA) wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sun fara yin kira da a duba yanayin da fursunoni suke ciki a gidajen kason Saudiyya.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, kungiyar kare hakkin bil adama a kasar Switzerland ta yi kira da a gudanar da bincike kan yanayin da gidajen kason Saudiyya, domin tabbatar da irin halin da fursunoni suke ciki, musamman ma fursunonin siyasa.

Wannan kira ya samu karbuwa daga kungiyoyin Kare hakkin bil adama da dama daga kasashen duniya, inda suke yin kira ga hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya da ta shiga gaba domin gudanar da wannan bincike.

Rahoton ya ce akwai bayanai da suke tabbatar da cewa, akwai dubban mutane da suke tsare a cikin mummunan yanayi, da suka hada da fursunoni na siyasa da kuma wadanda aka kama saboda banbancin mahanga ta mazhba, wadanda su ma suna cikin mawuyain hali.

Daga fitattun mutanen da suke tsare yanzu haka akwai Sheik Salman Audah, wanda shi ma yana daga cikin fitattun malaman masarautar Al Saud, amma yarima Muhammad Bin Salman ya bayar ad umarnin kame shi, tun shekara ta 2018, bisa zarginsa da neman a yi gyara a cikin salon siyasar da ke tafiyar da masarautar Al Saud.

Bisa wannan zargi kotun koli ta kasar Saudiyya ta zarge shi da cin amanar kasa, kuma ta yanke masa hukuncin kisa, wanda matsin lamabar kungiyoyin kare hakkin dan adam ne ya hana aiwatar da kisan har yanzu.

Baya ga 'yan syasa da malaman addini da masu fafutukar kare hakkokin 'yan kasa, akwai 'yan jarida dama da suke tsare, wasu daga cikinsu ma suna fuskantar hukuncin kisa, saboda yin rubuce-rubuce da ke sukar siyasar Muhammad Bin Salman, daga cikin irin wadannan 'yan jarida akwai marigayi Jamal Khasoggi, wanda shi ya samu damar ficewa daga kasar, amma duk da haka an tura jami'an tsaro sun kashe shi a ofishin jakadancin Saudiyya a kasar Turkiya shekaru biyu da suka gabata.

 

3950557

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :