IQNA

Firayi Ministan Canada Ya Yi Bayani Na Tunawa Da Musulmin Da Aka Kashe A Masallaci A Quebec

21:27 - January 30, 2021
Lambar Labari: 3485604
Tehran (IQNA) firayi ministan kasar Canada ya fitar da wani bayani na tunawa da musulmin da aka kashe a masallaci a garin Quebec na kasar.

Tashar CBC ta bayar da rahoton cewa, Justin Trudeau firayi ministan kasar Canada ya fitar da wani bayani na tunawa da musulmin da aka kashe a masallacin garin Quebec shekaru hudu da suka gabata.

A cikin bayanin nasa ya bayyana cewa, a kowace shekara ana fitar da bayani da kuma yin taro na tunawa da wadannan musulmi da aka yi wa kisan gilla a cikin masallaci, amma a wannan karon ya kudiri aniyar sanya wannan rana ta zama ranar tunawa da wadannan musulmi a hukumance a kasar Canada.

Ya ce sanya wannan rana ta zama ranar tunawa da su a hukumance yana hakan yana da matukar muhimamnci, domin kuwa hakan zai sanya wannan lamari na bakin ciki da takaici ya zama a raye a cikin zukatan dukkanin al’ummar Canada har abada.

Baya ga haka kuma sun cancanci hakan, domin kuwa an kashe sun ea  cikin masallaci a lokacin da suke yin ibada ba tare da sun yi wa kowa laifi ba, kuma hakan zai sanya a ci gaba da kara kyamar irin wanann aiki na ta’addanci da zalunci da nuna kiyayya ga musulmi.

A ranar 29 ga watan Janairun 2017 ne wani matashi mai tsananin kiyayya da musulmi ya shiga masallacia  Quebec ya budewa musulmi wuta  alokacin da suke salla, ya kashe 6 ya kuma jikkata wasu.

3950651

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :