A wata zantawa da ta yi da maneman labarai a jiya, Marine Le Pen shugabar jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya a kasar Faransa, kuma ‘yar takarar jam’iyyar a zabe mai zuwa, ta bayyana cewa tana bayar da shawarar kafa dokar hana saka hijabin muslunci ga mata a wuraren harkokin jama’a a kasar Faransa.
Tun kafin wannan lokacin dai Marine Le Pen dai ta bayyana ra’ayinta kan cewa, idan har ta samu nasarar lashe zaben shugaban kasar Faransa, to kuwa za ta hana saka sutura irin ta addinin muslunci a kasar.
A zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar Faransa a cikin shekara ta 2017, Marine Le Pen ta samu kuri’u miliyan 7.6 yayin da Macron ya samu miliyan 8.6.
A zabe zagaye na biyu da aka gudanar kuwa, ta samu kashi talatin da hudu ne cikin dari na dukkanin kuri’un da aka kada, wanda hakan ya bai Macron damar kayar da ita a zaben, inda zabe mai zuwa ake kallon cewa ita ce babbar barazana ga makomar shugabancin Macron a zabe mai zuwa.