Jami'an Tsaron Isra'ila Sun Tarwatsa Masu Adawa Da Gina Matsugunnan Yahudawa
Tehran (IQNA) jami'an tsaron Isra'ila sun tarwatsa daruwan falastinawa masu gangamin nuna adawa da gina matsugunnan yahudawa 'yan kaka gida a cikin yankunansu.
Jami'an tsaron Isra'ila a cikin shirin yaki sun tarwatsa daruwan falastinawa masu gangamin nuna adawa da gina matsugunnan yahudawa 'yan kaka gida a cikin yankunansu da ke yankin Dajana gabashin birninNablus.