Safin yada labarai na Sadal balad ya bayar da rahoton cewa, mabiya addinin kirista karkashin jagorancin daya daga cikin malaman addinin kirista na Arthodox a Masar Bolis Metri, sun taimaka ma musulmi wajen aikin sake gina wani masallaci a cikin lardin Qana.
Wannan yana daga cikin irin dabiun da musulmin wannan yankin suke nuna wa mabiya addinin kirista ne a lokacin da su ma suke taimaka musu a cikin dukkanin lamurransu.
Musulmi da kirista a wanan yankin suna zaune lafiya da juna a tsawon tarihinsu, kuma irin zumunci da taimakekeniya da ke tsakaninsu, tana a matsayin babban misali na fahimtar juna da girmama juna tsakanin mabiya wadannan manyan addinai guda biyu.