IQNA

23:01 - February 15, 2021
Lambar Labari: 3485654
Tehran (IQNA) musulmin kasar Faransa sun nuna rashin amincewa da dokar da ake shirin kafawa a kasar da sunan yaki da tsatsauran ra’ayi.

Tashar Aljazeera ta bayar rahoton cewa, wasu daga cikin musulmin kasar Faransa sun gudanar da gangami domin nuna rashin amincewarsu da dokar da ake shirin kafawa a kasar da sunan yaki da tsatsauran ra’ayi wadda ke nufin takura musulmi.

Musulmin kasar Faransa suna da imanin cewa, wannan dokar za ta takura su tare da kayyade harkokinsu na addini, da sunan hana yaduwar tsatsauran ra’ayi ko yaki da ta’adanci.

Wasu daga cikin musulmin na Faransa suna bayyana cewa, babban abin da yafi hadari a cikin wannan doka shi ne, tana a matsayin abin da yake halasta keta alfarmar addinin musulunci, tare da bayyana shi a matsayin addinin ta’addanci a hukumance.

Babban kwamitin musulmin kasar Faransa bai amince da daftarin wannan doka ba, kamar yadda manyan kungiyoyi da cibiyoyin musulmi da dama na kasar ba su amince da hakan ba, amma shugaban kasar Faransa ya kirayi wasu daga limamai ya tilasta su amincewa da samar da wannan doka.

3954090

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: