IQNA

Sakon Jagora Ga Taron Gamayyar Kungiyoyin Dalibai Musulmi A Turai

19:36 - February 20, 2021
Lambar Labari: 3485673
Tehran (IQNA) Ayatollah Sayyid Ali Khamenei Jagoran juyin juya halin muslunci na Iran da ya aike da sako ga taro karo na 55 na kungiyoyin dalibai musulmi a jami’ion kasashen turai.

Jojjatol Islam Ahmad Wa'izi ne ya karanta sakon na jagoran wanda ya aike zuwa ga zaman taron gamayyar kungiyoyin dalibai musulmi a jami’ion kasashen turai karo na hamsin da biyar.

A farkon sakon nasa:

Jagoran ya jadadda muhimmancin irin gudunmawar da matasa musamamn dalibai da suka yi karatu a fagagen ilimomi daban-daban suke bayarwa domin ci gaban al’umma da kuma gina ta a dukkanin bangarori.

Haka nan kuma ya yi ishara da abin da ya faru a wannan lokaci kimanin shekara guda ya zuwa na bullar cutar corona da kuma watsuwarta a duniya, ya nuna yadda matasa masu himma suka bayar da gudunmawa kuma suke ci gaba da bayarwa a bangarori daban-daban domin tunkarar wannan annoba.

Daga karshe ya ce matasa masu karatu a bangarori na ilimi a jami’oi daban-daban, wannan babbar dama ce da suke da ita, da kuma ya kamata su yi amfani da ita domin samun duk wani ilimi da zai ba su damar taimakon al’umma da kuma ci gabanta a dukkanin bangarori na rayuwa.

3955107

 

 

 

captcha