IQNA

19:41 - February 21, 2021
Lambar Labari: 3485677
Tehran (IQNA) wata majami’ar mabiya addinin kirista a garin Deton na jihar Texas, ta tattara taimakon kudade kimanin dala dubu 50 domin gyara wani masallaci a garin.

Shafin yada labarai na WFFA ya bayar da rahoton cewa, sakamakon guguwar iska mai tafe ruwa da kuma matsanancin sanyi da saukar dusar kankara mai yawa, ginin masallacin musulmi da yake hade da cibiyar muslunci ta (Denton Islamic Society) da ke garin Denton ya samu matsala.

Wannan yasa musulmi da kiristoci mazauna birnin suka fara tattara taimakon kudade domin ganin an gyara ginin masallacin da kuma cibiyar muslunci, inda cocin birnin ta hada taimakon kudade da ya kai dala dubu 50, ta mika ga kwamitin masallacin, domin a kara cikin kudin gyaran masallacin.

Faraz Kuraishi, shi ne shugaban cibiyar musulmin ta birnin Deton, ya bayyana cewa abin da ya faru abu ne mai faranta rai matuka, kuma wanann shi ne abin ya kamata ya kasance, zaman lafiya da fahimtar juna da girmama juna tsakanin dukkanin mabiya addinai, musamman musulmi da kirista.

Dalibai musulmi a jami’ar Texas ne suka gina wannan wuri ne a cikin shekara ta 1981, wada yake a matsayin masallaci na farko da aka gina a cikin jihar.

 

3955236

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: