IQNA

22:05 - February 22, 2021
Lambar Labari: 3485681
Tehran (IQNA) Allah ya yi fitaccen dan gwagwarmaya da zaluncin 'yan mulkin mallaka a kasashen musulmi da na larabawa Anis Naqqash rasuwa.

Allah ya yi fitaccen dan gwagwarmaya da mamayar Isra’ila a kasashen musulmi da na larabawa Anis Naqqash rasuwa a birnin Damascus na kasar Syria yana da shekaru 70 a duniya, bayan kamuwa da cutar Corona.

Anis Naqqash wanda dan kasar Lebanon, ya sadaukar da mafi yawan rayuwarsa ta kuruciya wajen gwagwarmaya da zalunci irin na Isra’ila da ma kasashe ‘yan mulkin mallaka.

Ya kasance tare da jagoran kungiyar kwatar ‘yancin kai ta Falastinawa wato marigayi malam Yasir Arafat, a  cikin harkokinsa na gwagwarmaya da zalunci da kuma mamayar Isra’ila a kan yankunan Falastinu.

3955566

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: