IQNA

18:01 - February 24, 2021
Lambar Labari: 3485685
Tehran (IQNA) ana saka tutoci da furanni a kan ginin hubbaren Imam Ali (AS) a daidai lokacin da ake shirin gudanar da tarukan tunawa da zagayowar lokacin haihuwarsa.

Cibiyar da ke kula da harkokon hubbaren Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf Ashraf a kasar Iraki, ta jagoranci saka tutoci masu launin fari da kore, da kuma furanni, domin murnar zagayowar lokacin haihuwarsa.

A kowace shekara ana gudanar da taruka na tunawa da wannan rana, tare da gabatar da jawabai a kan matsayinsa madaukaki, wanda miliyoyin masoya ahlul bait suke halarta daga ciki da wajen kasar Iraki, amma a shekarar bana an takaita halartar tarukan ga mutane kalilan, saboda yanayin da ake ciki na cutar korona a duniya.

 

 

 

3956031

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: