IQNA

Tehran (IQNA) cibiyar musulunci ta kasar Sweden ta nuna wasu tsoffin hotuna na hubbaren Imam Ali (AS).

A daidai lokacin da ake gudanar da tarukan tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Ali (AS) cibiyar musulunci ta kasar Sweden da ke birnin Stockholm ta nuna wasu tsoffin hotuna na hubbaren Imam Ali (AS) da aka dauka tsawon shekaru masu yawa da suka gabata.